CHECK AM FOR WAZOBIA

BINCIKEN GASKIYA: Yahaya Bello ya halarci taron da Tinubu yayi da gwamnoni?

BY Ahmad Sahabi

Share

Labarin cewa Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi, ya halarci taron da Shuganam kasa Bola Tinubu yayi da gwamnoni da wasu ministoci a fadar sa dake Abuje a ranar alhamis.

A taron, Tinubu da gwamnonin sun amince da bukatar karin daukan ‘yan sanda domin magance matsalar tsaro dake yaduwa a kasar.

Bayan taron, wani mai shafi a X ya tura hoton Bello a tsaye tare da sauran gwamnoni da Tinubu a fadar shugaban kasa.

“Yahaya Bello har yanzu ya na halartar zaman kwamitin zartarwa a matsayin gwamnan jihar Kogi duk da ya mika ma wani mulki,” inji rubutun.

Advertisement

Wadansu a shafin su na X suma sunce Bello ya halarci taron da Tinubu yayi da gwamnoni duk da ya mika mulki a watan Janairu.

A hoton dake yawo, ana iya ganin Yahaya Bello a tsaye a gefen Hope Uzodinma, gwamnan Imo da Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Legas da kuma Tinubu a tsaye a tsakiyan sauran gwamnoni sun zagaye shi.

Saidai, Yahaya Bello ya halarci taron?

Advertisement

Bello ne gwamnan jigar Kogi a karkashin jam’iyar All Progressives Congress (APC) daga 2016 zuwa 2024. Usman Ododo ne ya karba mulki daga Bello wanda aka rantsar a ranar 27 na Janairu.

A matsayin shi na tsohon gwamna, Bello ba shi da damar halartar taron gwamnoni da shugaban kasa; Ododo ne ko kuma mataimakin sa ne kawai zasu iya.

Binciken TheCable ya nuna hoton dake yawo, shafin fadar shugaban kasa na X ne suka fara tura hoton. Anyi amfani da hoton ne don yin bayanin abubuwan da aka tattauna a taron.

Tsohon hoton da ke yawo

Karin bincike ya nuna an dauka hoton ne a taron farko da Tinubi yayi da gwamnoni bayan ya zama shugaban kasa. Bello a lokacin shine gwamnan jihar Kogi.

Advertisement

Hoton tun watan Yuni ma 2023 aka dauke shi.

Sannan, kayan da shuagabannin suka saka a taron da suka yi bara ya banbanta da na taron da aka yi ranar alhamis.

Fadar shugaban kasa tuni ta chanza tsohon hoton da ta saka a shafin ta da hotunan da aka yi a ranar alhamis.

Ododo ya halarci taron kuma an dauke shi hotuna.

Shugaba Tinubu da gwamnoni a 15 na Febrairun 2024

Ododo na gaisawa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima kafun fara zaman taron gaggawa da Tinubu a 15 na Febrairu, 2024.

HUKUNCI

Duk da shafin fadar shugaban kasa na X ne suka fara tura hoton, maganar cewa Bello ya halarci taron gwamnoni da Tinubu a fadar shugabn kasa ranar alhamis ba gaskiya bane.

Advertisement

Ga ainihin hotunan da aka dauka a taron.

This website uses cookies.