CHECK AM FOR WAZOBIA

Shin Borno girman daya da UK da Sweden kamar yadda Osinbajo yayi ikirari?

BY Ahmad Sahabi

Share

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa jihar Borno tana da girman kasar Ingila (Birtaniya) da Sweden a hade ko kuma Burtaniya da Denmark.

Laolu Akande, mai magana da yawun Osinbajo, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasar ya tattauna da kungiyar daliban makarantar kasuwanci ta Harvard da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta.

Yayin da yake zantawa da daliban da suka yi Ziaran Bude-Ido Afirka, Osinbajo ya ce domin kasashen duniya su kara fahimtar girma da sarkakiyar kalubalen tattalin arziki da tsaro da Najeriya ke fuskanta, yana da kyau a yi la’akari da girman kasar.

“Na farko, akwai bukatar a yaba da girman kasar, wanda ke da matukar muhimmanci wajen fahimtar mene ne batutuwa.

Advertisement

“Misali, jihar Borno, girman ta kusan daya ne da gabadaya UK a hade da Sweden ko Denmark.

Saboda haka, idan akayi rahoto akan cewa akwai tashin hankali a Nijeriya, baze wuce a wani bangare daya na kasar ba, sannan mutane da yawa dake Abuja da Legas kila a shafun sada zumunta zasu ji, irin haka ne girman kasar nan.

“Idan ana maganan girman tattalin arziki, ana yawan hada mu da kananan kasashen Afurka, amma akwai jihohi guda 10 a Nijeriya da suka fi sauran kasashen girman GDP, babban kasuwa ne da za awa hari.”

Advertisement

Jihar Borno girman ta daya da gabadaya UK da Sweden ko Uk da Denmark idan aka hada su?

Labarin an buga shi a kafafen yada labarai daban-daban.

Tabbatarwa

Advertisement

TheCable ta duba griman jihar Borno, jihar dake Arewa maso gabashin kasar nan anyi ta ne a wata Febrairo 1976. An kara rabata a 1991, sanda aka fidda jihar Yobe daga cikin ta.

Jihar Borno, wadda akafi sanin ta da taken ‘Home of peace’, daga yammacin da jihar Yobe ce. Jihar Borno ta kuma hada iyaka da kasar Niger daga Arewacin ta, da kuma Chad daga Arewa maso yamma sannan daga gabas din ta kuma kasar Kamaru.

Ainihin shafin gwamnatin jihar Borno yace gaba daya girma da fadin jihar shine 61,435sqkm, inda ta zama itace jiha ta biyu a girma bayan jihar Niger.

A bayanan da ofishin kididdiga na kasa (NBS) da hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) na shekarar 2019 ya nuna cewa yawan mutanen dake jihar Borno sunkai mutane miliyan 5.7

United Kingdom ta hada da gabadaya Birtaniya, wanda ya kunshi Ingila, Wales da Scotland-tare da bangaren arewancin tsibirin Ireland.

Bayanan bankin duniya na 2021, ya nuna cewa girman United Kingdom yakai 241,930km2.

Advertisement

Ofishin kididdiga na UK, babban ofishi mai zaman kanta dake fidda sahihan kididdiga tace yawan mutanen dake UK mutane miliyan 67 ne.

Sweden ta na kan Scandinavian peninsula a arewacin nahiyar Turai. Babban birnin kasar Stockholm ne tun shekarar 1523. Sweden ce tafi kwashe girman Scandinavian Peninsula, wanda ita da Norway ke da iyaka.

Duka da kasar tana da tarihin shafe shekaru 1000 tana zaman kanta, fadin yanki bai chanza ba sai a shekarar 1809.

Bayanan bankin duniya na 2021 yana cewa girma da fadin kasar Sweden 407,310km2 sannan mutanen kasar miliyan 10.4 ne.

Denmark ita tana tsibirin Jutland, wanda ya miki har ta arewacin sa har zuwa tsakiyan nahiyar Turai ta yamma. Jutland ya kwashe kashi biyu cikin uku na girman kasar.

A shekarar 2021, bankin duniya ta bayyana girman Denmark a matsayin 40,000km2 da mutane yawan miliyan 5.8.

Jihar Borno, a girma tafi kasar Denmark, sannan yawan mutanen jihar kusan daya ne da yawan mutanen dake Denmark, amma akwai banbancin girma da yawan mutane tsakanin jihar Borno da Sweden da kuma United Kingdom.

Binciken da TheCable tayi ya nuna cewa girma da yawan mutane na United Kingdom kadai yafi na jihar Borno da nisa, balle a hada Uk da Sweden ko Denmark.

Borno United Kingdom  Sweden Denmark United Kingdom Sweden United Kingdom + Denmark
Landmass (km²) 61,435 241,930  407,310  40,000  649,240  281,930
Population 5,751,590 67,081,000 10,415,811 5,856,733 77,496,811 72,937,733

Hukunci

Maganan mataimakin shugaban kasa Osinbajo na jihar Borno girman ta daya da UK da Sweden a hade ko UK da Denmark a hade ba gaskiya bane, an zuzuta shi ne.

This website uses cookies.