Monday, December 5, 2022
MARKET UPDATE
Advertisement

TheCable

Advertisement
Cable Ads

Shin CBN ya gabatar da N5,000, N2,000 kamar yadda aka yi ikirari a wani bidiyo?

Shin CBN ya gabatar da N5,000, N2,000 kamar yadda aka yi ikirari a wani bidiyo?
November 19
08:05 2022

Wani bidiyo da ke nuna N5,000 da N2,000 ya kasance yana yawo a yanar gizo.

A cikin faifan bidiyon, wanda aka yada a shafin Twitter a ranar 27 ga Oktoba, wata mata ta nuna tarin kudi N5,000 da N2,000.

Matar tace wani mahaukaci ne ya zo ya ajiye shi a reshen bankin da take aiki.

“Ina fatan wannan wasa ne,” inji rubutun da akayi a kasan bidiyon wanda mutane sama da 33,000 suka kalla, mutane 1,028 sun danna like da kuma retweets 367.

Advertisement

An kuma yada ta a Instagram da kuma asusu da yawa a Facebook, inda ‘yan Najeriya da dama da ba a san ko su wanene ba suka nuna kaduwa da wannan ci gaba.

A ranar 26 ga watan Oktoba, Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya ce babban bankin ya sanar da sake fasalin wasu takardun kudi na Naira.

Emefiele ya ce sabon tsarin wanda ya hada da N200, N500 da N1000 zai fara aiki daga tsakiyar watan Disamba na 2022.

Gwanman CBN ya kare da cewa chanjin fasalin kudin sakamakon kalubalen da kasar ke fuskanta ne a bangaren kula da kudi dake kokarin bata mutuncin CBN da kasar.

Advertisement

Tabbatarwa

TheCable ta saka bidiyon a Invid, wani na’ura dake duba ingancin bidiyo, domin gudanar da bincike a bidiyon. Binciken ya nuna bidiyon ya dade yana yawo a Facebook da YouTube tun 2020.

Daga abun da ake gani, a gefe daya na N5000 din ana ganin hoton wani mutun sanye da hula, a dayan gefen kuma, hoton mata ne guda uku dake kusa da juna.

Binciken da akayi a Google ya nuna cewa a Agustan 2012, CBN ta sanar da shirin buga kudin N5,000.

Advertisement

Sanusi Lamido, gwamnan CBN a lokacin yace fuskokin manyan mata uku yan Nijeriya za a saka a sabon kudin wadan da suka hada da Margaret Ekpo, yar siyasa da ta mutu; Hajia Gambo Sawaba, yar siyasa da ta mutu, da Funmilayo Kuti, yar siyasa da ta mutu.

Lamido yace yin kudin N5000 zai kara wa kudin kasar inganci da kuma rage yawan kudin da ake biya wurin buga kudin.

Advertisement

Sai dai, biyo bayan maganar sa, aka yi ta sukar buga sabon kudi. Kungiyar ICAN tace idan CBN ta buga kudin N5000 zai rage wa naira daraja.

Gwamnatin Nijeriya, da farko ta amince, amma daga bisani ta dakatar da yin kudin N5000 domin “ta ba CBN lokaci ta sake yin bincike da nazari akan batun.

Advertisement

A ranar 31 ga watan Mayun 2020, CBN a shafin ta na Twitter, tayi kira ga yan Nijeriya da suyi watsi da hotuna da bidiyo na bogi da ke yawo a lokacin.

Sanusi Lamido, gwamnan babban bankin na CBN, ya ce fuskokin wasu fitattun ‘yan gwagwarmaya mata uku na Najeriya da za a yi amfani da su a wannan sabuwar takardar sun hada da Margaret Ekpo, tsohuwar ‘yar siyasa kuma mai wayar da kan jama’a; Hajiya Gambo Sawaba, tsohuwar ‘yar siyasa ce kuma ‘yar gwagwarmaya, da Funmilayo Kuti, marigayiya ‘yar siyasa kuma ‘yar fafutukar kare hakkin mata.

Advertisement

Lamido yace yin kudin N5000 zai kara wa kudin kasar inganci da kuma rage yawan kudin da ake biya wurin buga kudin.

Duk da haka, ci gaban ya gamu da koma baya da suka da yawa. Cibiyar da ke kula da Akantoci ta Najeriya (ICAN) ta ce bullo da takardar kudi na N5000 da CBN ta yi na iya kara janyo faduwar darajar Naira.

Gwamnatin Najeriya, duk da amincewar da ta samu a baya, ta dakatar da gabatar da N5000 don “baiwa CBN damar yin karin haske kan lamarin”.

Haka kuma, CBN ta shafinta na Twitter a ranar 31 ga Mayu, 2020, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da hotuna da bidiyoyin karya da ake yadawa a wancan lokacin.

“Bidiyo da hotunan da aka ce ana yadawa na N2,000:00 da Naira 5,000:00 karya ne kuma na bogi. An shawarci jama’a da su yi watsi da irin wannan karyar, kuma su kai rahoton duk wanda aka samu da irin wadannan takardun ga jami’an tsaro,” CBN ta wallafa a shafinta na Twitter.

Ana raba tsohon bidiyon a dandamalin kafofin watsa labarun a cikin tsammanin tsakiyar watan Disamba 2022 da aka sanar kwanan wata don sakin kudin da aka sake fasalin.

A halin da ake ciki, CBN ya sanar da sake fasalin N200, N500, da N1000, babban bankin bai taba bayyana wani shiri na gabatar da takardun kudi na N2000 ko N5000 ba.

Hukunci

Bidiyon da ake yadawa na cewa gwamnatin tarayya na gabatar da N2,000 da N5,000 karya ne. Bidiyon kudin bogin yana ta yawo a yanar gizo tun 2020.

0 Comments

No Comments Yet!

There are no comments at the moment, do you want to add one?

Write a comment

Write a Comment