CHECK AM FOR WAZOBIA

Shin farashin man fetur na Najeriya shi ne mafi arha a duniya kamar yadda Eniola Badmus ta yi ikirari?

BY Ahmad Sahabi

Share

Eniola Badmus, yar film ta Nollywood, tace dukda cire tallafin mai da akayi a baya, farashin man Nijeriya ne yafi na ko ina a duniya arha.

Yar film din, wadda sananniyar mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ce, tayi wannan maganan ne a wani shirin kai tsaye a Instagram wanda Daddy Freeze ya shirya.

Badmus ta ce da yawa daga cikin masu sukar gwamnatin Tinubu ba su san amfanin cire tallafin man fetur ba.

“A matsayi na ta yar kasa, ina da daman yin ra’ayi na, zan iya goyon bayan duk wanda nake so,” inji ta.

Advertisement

“Yawancin mayaƙan madannai ba su ma san menene tallafin mai ba. Sai da aka ma cire shi ne sannan suka san me gwamnatin takeyi. Har yanzu ma, inaga muna siyan mai dayafi ko wanne arha a duniya.

“Shugaba Tinubu yana nan. Bayan kasancewarsa mai goyon bayansa, na ga abin da ya yi kuma na san abin da zai yi. Ban taba ganin mai taimakon jama’a a matsayin shugabanmu na yanzu ba. Har ya bar ofis zan tsaya masa”.

CIRE TALLAFIN FETUR

Advertisement

A ranar 29 ga watan Mayu, shugaba Bola Tinubu a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na farko a matsayin shugaban kasa ya ce tsarin tallafin man fetur ya kare.

“Akan tallafin man fetur, abin takaici, kasafin kudin kafin na hau mulki shi ne babu wani tanadi da aka yi na tallafin man fetur. Don haka tallafin man fetur ya tafi,” inji shi.

Ya kara da cewa tallafin ba zai iya kara tabbatar da yadda ake kara kashe kudadensa ba sakamakon busar da albarkatun kasa.

“Mun yaba da matakin da gwamnatin mai barin gado ta dauka na kawar da tsarin tallafin man fetur wanda ya kara fifita masu hannu da shuni fiye da talakawa.

Advertisement

“A maimakon haka za mu sake mayar da kudaden zuwa mafi kyawun saka hannun jari a ayyukan jama’a, ilimi, kiwon lafiya da ayyukan yi da za su inganta rayuwar miliyoyin.

Jim kadan bayan sanarwar Tinubu, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa sama da Naira 500 kan kowace lita.

A ranar 18 ga watan Yuli, ‘yan kasuwar man sun sake kara farashin man fetur a gidajen sayar da man zuwa Naira 617 kan kowace lita a Abuja da kuma Naira 568 a Legas.

Shin da gaske ne man fetur na Najeriya shine mafi arha a duniya? TheCable ta duba farashin mai a fadin duniya kuma ga abun da muka samo.

NAZARI NA FARASHIN MAN FETUR A DUNIYA

A cewar Globalpetrolprices, shugaban kasuwar duniya wanda aka sani da bin diddigin farashin dillalan man fetur, wutar lantarki, da iskar gas a cikin kasashe sama da 150, ana sayar da mai a Venezuela kan farashi mafi arha a duk duniya. A halin yanzu farashin yana kan N3.1274 kowace lita.

Advertisement

Wani bincike da TheCable ta yi ya nuna cewa baya ga Venezuela, ana sayar da man fetur kasa da Naira 617 a wasu kasashe 20.

S/N Country Price in $ as of July 24 CBN Exchange rate on July 24 price in Naira
1. Venezuela 0.004 781.85 3.1274
2. Iran 0.029 781.85 22.67365
3. Libya 0.031  781.85 24.23735
4. Algeria* 0.34 781.85 265.829
5. Kuwait* 0.342 781.85 267.3927
6. Angola 0.364  781.85 284.5934
7. Egypt* 0.372 781.85 290.8482
8. Turkmenistan 0.429 781.85 335.41365
9. Malaysia* 0.448 781.85 350.2688
10. Kazakhstan 0.488  781.85 381.5428
11. Bahrain 0.531  781.85 415.16235
12. Bolivia* 0.542  781.85 423.7627
13. Iraq 0.573  781.85 448.00005
14. Qatar* 0.577  781.85 451.12745
15. Azerbaijan 0.588  781.85 459.7278
16. Russia* 0.589 781.85 460.50965
17. Oman* 0.621 781.85 485.52885
18. Saudi Arabia* 0.621 781.85 485.52885
19. Ecuador* 0.634 781.85 495.6929
20. Kyrgyzstan* 0.741 781.85 579.35085
21. Afghanistan 0.743 781.85 580.91455
22. Nigeria 0.778 781.85 608.2793
23. UAE* 0.787 781.85 615.31595
24. Tunisia 0.832 781.85 650.4992
25. Bhutan 0.845 781.85 660.66325
26. Lebanon* 0.863 781.85 674.73655
27. Indonesia* 0.864 781.85 675.5184
28. Colombia* 0.867 781.85 677.86395
29. Pakistan* 0.878 781.85 686.4643
30. Argentina* 0.924 781.85 722.4294
31. Belarus* 0.935 781.85 731.02975

Kasashen sun hada da; Iran, Libya, Aljeriya, Kuwait, Angola, Masar, Turkmenistan, Malaysia, Kazakhstan, Bahrain, Bolivia, Iraq, Qatar, Azerbaijan, Russia, Oman, Saudi Arabia, Ecuador, Kyrgyzstan, da Afghanistan.

Ya kamata a lura cewa kasashe 19 daga cikin 23 suna sayar da man fetur kasa da Naira 568 kan kowace lita, wanda ake ganin shi ne mafi arha a Najeriya a yau.

HUKUNCI

Shahararriyar ‘yar fim din ta ce man fetur din Najeriya ne mafi arha a duniya karya ne. Yanzu haka kasashe 19 na duniya suna sayar da man fetur kasa da farashin famfo N568 a Legas.

Ga wannan rahoto, chanjin dollar zuwa naira yana kan $1=781.85 a cewar babban bankin yankin (CBN) ya zuwa ranar 24 ga Yuli, 2023, lokacin da jarumar ta yi ikirarin.

This website uses cookies.