MARKET UPDATE
Advertisement Topt

TheCable

Wani lauya yace mace ta daukan ma wata matar ciki karya doka ne a Najeriya. Gaskiya ne?

Wani lauya yace mace ta daukan ma wata matar ciki karya doka ne a Najeriya. Gaskiya ne?
May 09
11:28 2024

Sonnie Ekwowusi, wani lauya, yace mace ta daukan ma wata matar ciki karya doka ne a Najeriya.

Ekwowusi yayi maganan ne a ranar 22 na Afrilu a hira da yayi a tashar Arise TV.

Yace mace ta daukan ma wata matar ciki “kamar hayan mahaifa ne” sannan a bayar da dan da aka haifa. Ya kara da cewa mace ta daukan ma wata matar ciki abune da ke matukar tauye ma mata mutuncin su.

“Da farko dai, mace ta daukar ma wata matar ciki ya saba ma yanayin hallita da kuma doka a Najeriya. Mutane da yawa basu sani ba cewa mace da daukan ma wata matar ciki a Najeriya karya doka ne ba,” inji shi.

Advertisement

Ekwowusi yace sashi na 30, karamin sashi na (1) a dokokin kare yara zai mara ma maganar sa baya.

Ya ce sashi na 3 ya tanaji hukuncin daure wanda ya karya shi na tsawon shekara 10 a gidan gyaran hali.

“Babu wanda zai iya siya, sayarwa ko hayan yaro,” inji sashin.

Advertisement

Biyo bayan maganar da yayi, yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakin su a kan fahimtar su na abin da doka ya ce a kan mace ta daukan ma wata matar ciki.

Advertisement

ME DOKAN NAJERIYA YACE A KAN MACE TA DAUKAN MA WATA MATAR CIKI?

Kasashe da yawa har yanzu basu bayyana nasu ra’ayin ba a kan batun ba, kuma, a Najeriya ma babu doka da ya hana.

A 2016, an shigar da wani kuduri a majalisar dokoki da zai kula da haihuwa ta amfani da na’urori na zamani amma kuma, kudurin bai zama doka ba. Saidai, jihar Legas ta fitar da wasu ka’idoji da suka shafi haihuwa.

Duk da cewa babu yawan adadin matan dake daukan ma wasu matan ciki a Najeriya, shaidu sun nuna cewa ana yi a Najeriya.

TABBATARWA

Don tabbatar da maganar da Ekwowusi yayi, TheCable ta tattauna da wasu lauyoyi don jin ta bakin su a kan batun.

Henry Akanwa, wani lauya, yace za iya yima mace ta daukan ma wata matar ciki kallan ta saba ma doka idan har an biya wanda ta da dauka cikin, inda ya kara da cewa yin hakan kaman “safaran yara ne”.

“Mace ta daukan ma wata matar ciki ba karya doka bane a Najeriya, saidai idan za a biya kudi ne ko kuma a siya yaron da aka haifa. Hakan zai iya zama safaran yara,” inji Akanwa.

“Idan mutum ya haifa yaro ba tare da aure ba kuma yayi niyyan bayar da yaron da aka haifa, wasu iyalin na iya karban yaron su rike a matsayin nasu ta bin hanyoyin da doka ta tanadar. A nan za a iya cewa macen da ta daukan ma wata matar cikin ce wanda ta haifa dan saboda ita ta haifa dan sannan ta bada shi.”

Olu Daramola, wani babban lauya, yace mace ta daukan ma wata matar ciki ba karya doka bane a Najeriya saboda babu doka da ya hana.

Yace abun da doka ne ya hana kawai za a kira shi karya doka idan an aikata shi.

Shima da yake magana a kan batun, Olutumbi Babayomi, wani lauya, yace baza a iya gurfanar da mutun a kotu ba a kan karya “dokan da babu shi ba”.

Awa Kalu, wani lauya, shima yace mace ta daukan ma wata matar ciki ba karya doka bane.

HUKUNCI

Babu doka da ya hana mace da daukan ma wata matar ciki a Najeriya. Dokokin kare yara dana kare lafiyar yara basu hana ba a Najeriya.

Click on the link below to join TheCable Channel on WhatsApp for your Breaking News, Business Analysis, Politics, Fact Check, Sports and Entertainment News!

Tags

0 Comments

No Comments Yet!

There are no comments at the moment, do you want to add one?

Write a comment

Write a Comment

error: Content is protected from copying.