General

Ya gaskiyan maganganun Tinubu da Shettima akan yawan tattalin arzikin jihar Legas?

BY Ahmad Sahabi

Share

Kashim Shettima, dan takaran mataimakin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yace jihar Legas ce ta uku a girman tattalin arziki a Afrika.

Tsohon gwamnan jihar Borno yayi wannan furucin ne ranar litinin a wurin taron shekara shekara na Nigerian Bar Association (NBA), inda ya wakilci Tinubu, dan takaran shugaban kasa a jam’iyar APC.

Dayake jawabi game da Tinubu da kuma bada dalilan da suka sa yake ganin cewa Tinubu yafi sauran yan takaran, yace jihar Legas ce ta uku a girman tattalin arziki a jihar Legas.

“Sanda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yazama gwamna a jihar Legas a 1999, abubuwan taimako cikin gaggawa na ambulance daya ne kawai a jihar wanda mallakin gwamnatin jihar ne. Jihar Legas na samun naira miliyan 700 a wata a kudaden da take hadawa a cikin jihar,” inji shi.

Advertisement

“A yanzu, jihar Legas na hada naira biliyan 50 duk wata, Lagos ce ta uku a girman tattalin arziki,” Shettima ya kara da cewa.

Amma ba wannan ne karo na farko da abokin tafiyan Tinubu yayi wannan maganan ba.

Advertisement

A wani bidiyo dayayi yawo a Twitter a ranar 5 ga watan Agusta, Shettima yace: “Abun da Nijeriya ke bukata yanzu shine shuagabanni da zasu ci gaba. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mutum ne da anyi ya gani, Legas ce ta uku a girman tattalin arziki a Afurka”.

Bidiyon wani mai shafin @Progressive4BAT, a Twitter ya fara tura shi, inda sama da mutum 130,000 suka kalla.

A ranar 6 ga watan Agusta, Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da ya tura bidiyon a shafin sa na Twitter, wanda kuma shine mai magana da yawun kungiyar yakin neman zabe na Tinubu, tare da rubutun: “kayi daidai yallabai”.

Advertisement

Tinubu ya taba kiran Legas ‘inda tafi ko ina girman tattalin arziki a Afurka.

A watan Afrilu 2022, Tinubu ya gana da kakakin majalisu ‘yan jam’iyar APC a wani taro da majalisar jihar Legas ta shirya.

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, Tinubu- yayin da yake tallata kansa kafun gudanar da zaben fidda gwani- yace a lokacin gwamnatinsa jihar Legas ta zama inda tafi ko ina girman tattalin arziki a Afrika.

“Na girma nazama mutum maras tsoro kuma wannan abun yana mun aiki. Babu kudin shiga dake shigowa da ga wurin gwamnatin tarayya FAAC, na kawo ci gaba a Legas kuma a yau, jihar tazama na daya a tattalin arziki a Afrika. Na ajiye daman yin kuri. Ina so nayi irin wannan aikin idan na zama shugaban kasan Nijeriya,” yadda aka ce Tinubu ya ce.

Shin Legas bata samu kudin shiga daga wurin gwamnatin tarayya ba daga 1999 zuwa 2007?
Yan takaran shugaban kasa da mataimakin sa- Tinubu da Shettima- sunyi gaskiya akan girman tattalin arzikin jihar Legas?

Ga abun da muka gano.

Advertisement

Shin Legas bata samu komai a kudin shiga daga gwamnatin tarayya ba a lokacin mulkin Tinubu?

A ranar asabar, 27 ga wata Maris, 2004, an gudanar da zabe domin hada kananan hukumomi guda 57 kamar yadda dokokin jihar Legas na sashi na 5 shekarar 2002 yace.

Jihohin Ebonyi, Katsina, Nasarawa, da Niger suma sun kafa kananan hukumomi a lokacin tare da Legas.

Tsohon shuganan kasa Olusegun Obasanjo a wata wasika da ya aikawa Nenadi Usman, karamar ministan kudi a lokacin mulkin sa yace: “Yadda ‘majalisa basu riga da sun gama tsare tsaren su na kafa sabbabin kananan hukumomi ba, gudanar da zabe a karkashin su ko bada bada kudin yi daga asusun gwamnatin tarayya zai zama saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan.

“Saboda haka, ka a baiwa kananan hukumomi a wadannan jihohin kudi daga asusun gwamnatin tarayya ko wata jiha data fado a cikin masu son karin kananan hukumomi, har sai sun koma yadda suke a yawan kananan hukumomin su kamar yadda yake dauke a cikin sashi na 1 a kundin tsarin mulkin kasarnan.

Biyo bayan umarnin da gwamnatin tarayya na dakatar da baiwa kananan hukumomi a jihohin da hanin ya shafa, sauran jihohin sun koma yadda suke amma banda Legas, ita takai kara zuwa kotu.

Yemi Osinbajo, attorner-janar na Legas, ya musanta cewa Obasanjo, cikin sashi na 162 kasan sashi (4) da (5) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, zai iya zartar da abubuwan da suka shafi gudanarwa ne ba na dokoki ba na dakatar da kudaden kananan hukumomi daga asusun gwamnatin tarayya.

Kotun koli a hukuncin ta, tace shugaban kasa baida daman hana kananan hukumomi 20 kudi ba. Ta bada umarnin a sake wa kananan hukumomi kudaden su.

Amma hukunci kotun bai shafi sabbin kananan hukumomin da jihar Legas tayi ba.

Duk da hukuncin kotun, gwamnatin tarayya ta rike kudin kananan hukumomin jihar daga watan Afrilu 2004 har zuwa karshen mulkin Tinubu da Atiku. Kudaden kananan hukumomin an basu daga baya da Umaru Musa Yar’adua ya zama shugaban kasa.

TheCable tayi magana da Muda Yusuf, tsohon daracta-janar na LCCI a Legas domin tabbatar da ko jihar bata samu komai daga jihar Legas bata samu komai daga wurin gwamnatin tarayya.

Kananan hukumomi ne ba a baiwa komai ba, banda jihar,” inji shi.

Wasu bayanai daga babban bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa Legas ta karba naira biliyan 11.7 na kudin alawus daga wurin gwamnatin tarayya a shekarar 2001. Bayanai dayawa dake hannun CBN wanda zasuyi bayanin kudaden da gwamnatin tarayya ta bawa Legas tsakanin 1999 da 2007 sanda Tinubu ke gwamna babu su a yanzu.

Daga bayanai daga ofishin akanta-janar na kasa (OAGF), BudgIT, a cikin littafin su da tarin bayanai na jihar da aka buga a 2018, ya nuna cewa Legas ta karba naira biliyan 48.62 a shekarar 2007, shekarar da wa’adin Tinubu ya kare.

Hukunci

Babu wani lokaci a mulkin Tinubu da aka hana jihar Legas kudi daga asusun gwamnatin tarayya, kudaden kananan hukumomi ne kawai aka dakatar daga shekarar 2004 zuwa 2007.
Maganan cewa jihar Legas an daina bata kudi ba gaskiya bane.

Kudin da Legas ke hadawa duk wata a shekarar 1999 naira miliyan 700 ne kamar yadda Shettima ya fada?

Shettima yace Legas ta samu naira miliyan 700 a kudaden da take hadawa na cikin gida a shekarar 1999 sannan a yanzu tana samun naira biliyan 51 duk wata. Ga abun da muka samo.

A cewar wasu baya daga CBN inda aka wallafa a binciken wata makaranta mai sunan “Research Academy of Social Sciences”, Legas ta hada naira biliyan 14.6 a shekarar 1999, wanda idan aka rarraba shi ze zama kusan naira biliyan 1.2 duk wata.

Hakan ya saba wa naira miliyan 700 din da Shettima ya ce da kuma naira miliyan 600 dake ta yawo a kafafen watsa labarai.

Da Tinubu ya sauka daga mulki a 2007, yawan kudin ya haura zuwa naira biliyan 83.02, a wata kusan naira biliyan 6.9. Tsakanin 1999 zuwa 2007, kudin da Legas da tarawa daga cikin gida ya haura inda yakai zuwa kashi 468.63.

Akinyemi Ashade, tsohon kwamishinan kudi na jihar Legas, yace a 2018 kudin da Legas ke hadawa a cikin gida naira biliyan 34 ne.

Ta sabon bayanai da cibiyar kiddidiga ta kasa (NBS) ta saka kwanaki, rahoton rabin shekara ya nuna cewa Legas ta hada naira biliyan 267 a cikin watanni shidan farko na 2021, idan aka raba shi duk wata zai kai naira biliyan 44.5- ba naira biliyan 51 kamar yadda shettima yace ba.

Hukunci

Kudaden da Legas ke hadawa na cikin gida duk wata da Tinubu yazama gwamna ba naira miliyan 600 bane kamar yadda yake yawo a kafafen watsa labarai kuma ba naira miliyan 700 bane kamar yadda shettima yace. Duk maganan yawan kudin ba daidai bane.

Legas ne mai yawan girman tattalin arziki na uku a Afurka?

TheCable ta duba maganan Shettima da Tinubu akan girman tattalin arzikin Legas. Shettima yace ita ce ta uku a girma a Afurka, Tinubu kuma yace itace tafi girma.

Don auna girman kowane tattalin arziki, Muda Yusuf , tsohon darakta-janar na LCCI, ya ce babban abin da ake samu na cikin gida (GDP) ya kasance ɗaya daga cikin ma’auni mafi aminci don sanin girman tattalin arzikin.

“GDP ga kowane mutum wanda ke raba GDP da yawan jama’a wani ma’auni ne saboda yana nuna jin dadin jama’a,” in ji shi.

“Lagos ba ta da wadata kamar yadda mutane ke faɗi saboda nauyin da ke wuyan yana da yawa idan kun danganta dukiyar wannan rukunin ga jama’ar da ke buƙatar kulawa. Kuma abin tambaya a nan shi ne, yaya mutanen da ke cikin tattalin arzikin suke da kwanciyar hankali?

A cikin 2020, Ofishin Kididdiga na Legas (LBS) ya sanya manyan biranen Afrika mafi arziki ta GDP a cikin daloli. Legas, mai GDP na dala biliyan 76 a matsayi na 4. Alkahira mai GDP na dala biliyan 212 ita ce mafi girman tattalin arzikin birni a Afirka sai Johannesburg (dala biliyan 131) sai Cape Town (dala biliyan 121).

Idan Legas kasa ce

Duk da kasancewar kasa mafi girman tattalin arzikin Afrika, GDP na jihar Legas ana kwatanta shi da sauran kasashen Afrika kamar kasa ce.

A cikin rahotonta na 2021, LBS ta bayyana cewa GDP na Legas ya kai N26.59 tiriliyan, kwatankwacin dala biliyan 61.9 ta hanyar amfani da kudin musaya na N429.43 da dala biliyan 38.4 ta hanyar amfani da ƙimar kasuwa N692 na yanzu.

TheCable ta kwatanta Legas da sauran ƙasashen Afrika ta amfani da bayanan 2021.

S/N Country GDP USD billion
1. Nigeria $440.7 billion
2. South Africa $419.9 billion
3. Egypt $404.1 billion
4. Algeria $167.9 billion
5. Ethiopia $111.2 billion
6. Kenya $110.3 billion
7. Ghana $77.5 billion
8. Angola $72.5 billion
9. Cote d’Ivoire $69.7 billion
10. Tanzania $67.7 billion
11. Lagos  $61.9 billion (Official rate)
12. Congo $53.9billion
13. Cameroon $45.2 billion
14. Uganda $40.4billion
15. Lagos $38.4 billion (Parallel market)
16. Sudan $34.3 billion
17. Senegal $27.6 billion

Yin amfani da adadin musaya a hukumance wajen sauya lambobin GDP da LBS da NBS suka bayar, Legas ta kasance ta 11 a Afrika kuma ta 16 tana tafiya daidai da farashin kasuwa. Alkaluman GDP na sama sun fito ne daga Bankin Duniya, ban da Legas, wanda aka ciro daga LBS.

Hukunci

Legas ba ita bace ta uku a Afurka a girman tattalin arziki ba kamar yadda Tinubu da Shettima sukace, idan aka hada ta da wasu manyan garuruwa a nahiyar, gwamnatin jihar ita kanta, tace jihar ce ta hudu a girman tattalin arziki a Afrika.

This website uses cookies.