Thursday, May 23, 2024
MARKET UPDATE
Advertisement Topt

TheCable

Amfani da fasahar kirkirar ruwan sama ne ya janyo ambaliyan ruwa a Dubai?

Amfani da fasahar kirkirar ruwan sama ne ya janyo ambaliyan ruwa a Dubai?
May 04
10:24 2024

Labarai da dama a shafukan sada zumunta na cewa amfani da fasahr kirkirar ruwan sama wanda ake kira “cloud seeding” ne ya janyo ambaliyar ruwan da a ka yi a United Arab Emirates (UAE).

Labarin, wanda ya bulla a X, Facebook, da Instagram, na cewa UAE na dandana kudar su ne na hada ruwan sama da suke yi.

Advertisement

 

Advertisement

RUWAN DA BA A TABA YIN IRIN SHI BA A TARIHIN DUBAI

A ranar 17 na watan Afrilu, wasu bangarori na Dubai na rufe da ruwa saboda ruwan sama mai yawan na shekara daya da aka yi inda ya janyo ambaliya sannan a ka bar motoci a kan hanyoyi.

Advertisement

Ruwan saman ya dakatar da aiki a tashan jirgin sama sannan ya janyo mutuwar mutane 19 a Oman, sannan kuma a ka sanar da bacewar mutane biyu.

Dubai na daya daga cikin garuruwan da ke karkashin UAE.

Advertisement

UAE a zagaye take da yashi kuma tana da locakin zafi da sanyi a shekara. Lokacin zafi yakan fado ne a tsakanin watan Juni zuwa Satumba. Lokacin sanyi kuma yakan fado daga Disamba zuwa Maris. Watan Janairu yafi zama lokacin da yafi ko wanne sanyi.

Masana sunce tun 1949 da aka fara gwada yawan ruwa da ake yi, bana ne karo na farko da a ka yi ruwan sama da ambaliya mai yawa.

Advertisement

MENENE FASAHAR KIRKIRAR RUWA (CLOUD SEEDING)?

Fasahar kirkirar ruwa wani hanyar samar da ruwan sama ne za ake zuba gishiri da wasu sinadirai a girgije don samun ruwan sama. Kasashe irin su UAE wadansu lokuta suna amfani da fasahar don samar da ruwan sama.

FASAHAR KIRKIRAR RUWA ZAI IYA JANYO IRIN WANNAN RUWA MAI YAWA?

Duk da cewa fasahar kirkirar ruwa na taimakawa a samar da ruwan sama, masana sunce ba zai iya hada girgije ba.

A wani hira da GB News, Maarten Ambaum, wani masani dake jami’ar Reading, yace UAE ba ta da tsarin samar da ruwan sama mai yawan da a ka yi a ranar 17 na watan Afrilu.

Ya kuma ce an dade ba a yi amfani da fasahar kirkirar ruwa ba a kasar saboda masana ta bincike sun gano ceww za a samu wadataccen ruwa.

TABBATARWA

TheCable ta tattauna da Taiwo Ogunwumi, wani masani a kan harkar ambaliyan ruwa, inda ya bayyana mana cewa za a iya alakanta ruwan da akayi da ayyukan dan Adam na yau da kullum.

Itama da take magana a kan lamarin, Gloria Okafor, wata malamar jami’ar Nigerian Maritime, dake jihar Delta tace ruwan da aka yi a UAE yafi karfin a ce ta amfani da fasahar kirkirar ruwa a ka yi.

HUKUNCI

Babu shaida ko wani abu da zai tabbatar da maganar cewa amfani da fasahar kirkirar ruwan sama ne ya janyo ambaliyan ruwan da akayi.

Click on the link below to join TheCable Channel on WhatsApp for your Breaking News, Business Analysis, Politics, Fact Check, Sports and Entertainment News!

Tags

0 Comments

No Comments Yet!

There are no comments at the moment, do you want to add one?

Write a comment

Write a Comment

error: Content is protected from copying.