CHECK AM FOR WAZOBIA

Binciken Gaskiya: A’a, ba Osimhen ne ke atisaye tare da sarkoki, tayoyi 

BY Ahmad Sahabi

Share

Victor Osimhen na daya da ga cikin ‘yan kwallon Najeriya da ke nuna kansu a gasar AFCON a kasar Ivory Coast. Duk da de kwallo daya kachal ya saka a raga a gasan, yana cikin masu yi ma Najeriya kokari.

Yayi kokari sosai a wasan da Najeriya ta buga da kasar Kamaru da ci biyu, inda ya ba Ademola Lookman kwallo ya zura kwallon karko da Najeriya taci a wasan a cikin raga.

Biyo bayan wasan Kamaru, ‘yan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta suna ta yada wani bidiyo na wani da ake cewa Osimhen ne yana yin atisaye.

A bidiyon, mutumin da ake gani a ciki, ya na yanayi da Osimhen yana atisaye da sarkoki da tayoyi da kuma abubuwan kankare.

Advertisement

“Kuna so ku san me yasa Osimhen ke da karfi? Kalli yanda ya ke yi atisaye,” Nkirukamma, wani mai shafi a X, ya rubuta a shafin sa a tare da bidiyon.

Mutane sama da 291,000 sun gani kuma sun karanda sannan dubban mutane sun danna alaman so a X(wanda aka fi sani da Twitter a da).

An tura bidiyon a shafuka daban-daban sannan har a Whatsapp ma an tura shi.

Advertisement

TABBATARWA

Advertisement

TheCable tayi bincike a kan bidiyon ta gano wani mai suna Ebube David ne a ciki.

David – wanda shine a cikin bidiyon ya na atisaye da sarkoki da tayoyi – na da mabiya sama da 190,000 a TikTok sannan ya yi fice a kwaikwayon Osimhen.

Ya daura bidiyon on ranar 13 na Disamban 2023, tare da rubutun: “Victor Osimhen ya dage kafun ya cimma burin sa, kuma zaku iya.”

HUKUNCI

Mutumin da ake gani a bidiyon ba Osimhen bane, Ebube David ne. Maganar cewa Osimhen ne ke atisaye a bidiyon karya ce.

Advertisement

This website uses cookies.