MARKET UPDATE
Advertisement Topt

TheCable

BINCIKEN GASKIYA: Kamfanin Shell zasu dakatar da aiki Najeriya?

BINCIKEN GASKIYA: Kamfanin Shell zasu dakatar da aiki Najeriya?
January 23
05:31 2024

Yayin da kamfanin Shell suka sanar da cewa zasu dakatar da aikin nema da hakar mai a ruwa a Najeriya, mutane da dama a shafukan sada zumunta suna ta cewa kamfanin man Birtaniya zasu fice daga kasar nan.

Da suke magana a kan sanarwar da Shell sukayi, wadansu yan’ Najeriya a shafukan sada zumunta sun tofa albarkacin bakin su, kuma wadansu daga cikin su, maganganun su ba daidai bane.

Wadansu maganganun da akayi sama da mutane dubu sun gani kuma sun yada a X, cewa Shell zasu dakatar da aiki a Najeriya inda suka shafe sama da shekara 80 suna aiki a kasar.

“Shell sun sanar cewa zasu fice daga Najeriya. Me turawa suke hangowa ne da mu bamu hango ba?” inji @Naija-Activist, wani mai shafi a X.

Advertisement

Wani mai shafi ma suna, @_Pheranme ya saka labarin a shafin sa tare da yin tambayan: “Wai meke faruwq da Najeriya ne?”

Shima wani da sunan shafin sa @ThisIsNot1967_, yace “Shell BP zasu fice daga Najeriya bayan sunyi shekara 85”.

Advertisement

WARWARE ZARE DA ABAWA

Da suke sanar da sauye-sauye a yanayi kasuwancin su a Najeriya, kamfanin sunce saboda wasu dalilai, zasu sayarda kamfanin su na samar da mai.

Renaissance – hadin gwiwa na kamfanoni biyar zasu siya kamfanin suci gaba da samar da mai.

Kamfanonin sun hada da ND Western, Aradel Energy, First Exploration da Production (First E&P), Waltersmith, da Petrolin.

A wata sanarwa da suka fitar a kan dakatar da aiki a teku, Shell sunce sayar da daya daga cikin kamfanonin su baya nufin zasu fice da Najeriy, inda kuma suka yi bayanin suna da wasu “manyan kamfanoni uku” a kasar.

A ci gaba da bayani, shell sunce suna rike da 25.6% a NLNG, da ke samar wa da kuma fitar da iskan gas zuwa waje.

DALILAN DA SUKA SA SHELL ZA SU DAINA AIKI A KAN RUWA

Niyan Shell na saida kamfanin su da ke aiki a ruwa abu ne da aka dade ana hangowa, inda kamfanin sun samu matsaloli na zubewar mai saboda satar mai, wadanda ke janyo musu kashe manyan kudade wurin yun gyara da kuma maka su a kotu.

Yawan maka su a kotu da ake ya hana su daman sayar da kadarorin su na saman ruwa.

A wani taron shekara-shekara a 2021, Ben van Beurden, tsohon mai kula da harkokin Shell, yace kamfanin na tattaunawa da gwamnatin tarayya domin sayar da kadarorin su na saman ruwa.

A Maris na 2022, wata kotun daukaka kara a Owerri ta dakatar da Shell daga sayar da duk wani kadara a Najeriya har sai an gama shari’an da ake na tarar $2 biliyan da aka ci kamfanin saboda zuberwar mai da ake zargi.

KAMFANONI KASASHEN WAJE NA TA SAIDA KADARORIN SU NA SAMAN RUWA

Wadansu kamfanonin kasashen waje suma sun sayar da kadarorin su na saman ruwa.

A Febrairu na 2022, Seplat Energy Plc ta amince ta saya gaba daya jarin ExxonMobil.

Saidai, har bayan sama da shekara daya, ba a kammala cinikin ba saboda wasu dalilai.

A Afrilu na 2022, TotalEnergies sun sanar da shirin su na sayar da jarin su na Najeriya.

Suma, Oando, a Satumba na 2023, suka sanar da sun kammala sayan kashi 100 na hannun jarin wani kamfani.

HUKUNCI

Maganar cewa kamfanin Shell zasu fice da Najeriya ba gaskiya bane. Shell zasu ci gaba da yin kasuwanci a Najeriya a wasu kamfanoni da suke da guda uku.

Click on the link below to join TheCable Channel on WhatsApp for your Breaking News, Business Analysis, Politics, Fact Check, Sports and Entertainment News!

0 Comments

No Comments Yet!

There are no comments at the moment, do you want to add one?

Write a comment

Write a Comment

error: Content is protected from copying.